<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Akwai haske yanzu cikin zuciyata
 Tun Yesu ya zo wurina.
 Aka gafarta mini duk zunubina
 Tun Yesu ya zo wurina.

[V2]
 KORUS
 Tun Yesu ya zo wurina,
 Tun Yesu ya zo wurina,
 Ina da kwanciyar rai,
 Har da murna sosai,
 Tun Yesu ya zo wurina.

[V3]
 2) Yanzu dai na ke da tabbataccen bege,
 Tun Yesu ya zo wurina.
 Wata rana zan zauna tare da shi can,
 Tun Yesu ya zo wurina.
 KORUS

[V4]
 3) Ɗanuwa, kana so ka yi murna kuma?
 Bar Yesu ya cece ka yau.
 Za ya gafarta maka duk zunubanka.
 Bar Yesu ya cece ka yau.

[V5]
 KORUS NA ƘARSHE
 Bar Yesu ya cece ka yau,
 Bar Yesu ya cece ka yau,
 Za ka yi kwanciyar rai,
 Har da murna sosai,
 In Yesu ya cece ka yau.</lyrics>
<title>Akwai Haske Yanzu Cikin Zuciyata LW155</title>
<hymn_number>155</hymn_number>
</song>